Birnin kebbi: Kotu ta sake tura matar da ake zargi da ajiye karamar yarinya zuwa Kurkuku

Rundunar yansandan jihar Kebbi ta gurfanar da wata mata mai suna Saratu Tukur Zaria a gaban wata babban Kotun Sharia na 4 da ke babban Kasuwar garin Birnin kebbi ranar Juma'a bisa tuhumar ajiye karamar yarinya ba bisa ka'ida ba a gidan da take haya a kusa da Otal na Galaxy a bayan unguwar tsohuwar tashar mota a garin Birnin kebbi.
.

Da karfe 11:19 na safiya, dansanda mai gabatar da kara Safeton yansanda Ahmed Sani mai lambar aiki 226780, ya shaida wa Kotu cewa a ranar 17 ga watan 10, 2019, an kama Ramatu Muhammad a dakin Saratu Tukur Zaria, kuma ana zarginta da sa yarinyar aikata alfasha.

Bayan Alkalin Kotun Mai sharia Sanusi Sidi Gazali ya tambayi Ramatu ko haka zancen yake? Ramatu ta musanta haka, sai dai ta gaya wa Kotu cewa ba haka zancen yake ba, ta kuma yi wa Alkali karin bayani.

Hakazalika Alkali Sanusi, ya tambayi wacce ake kara watau Saratu, ko haka zancen yake? ita ma Saratu ta yi wa Kotu bayani yadda Ramatu ta sameta har ta ajiye ta tsawon kwana biyu, da kuma abin da ya faru a wannan lokaci, da kuma yadda ta je har garin Jega domin neman mahaifiyar Ramatu.

Kotu ta tambayi mai gabatar da kara ko akwai wani abu da zai gaya wa Kotu ganin cewa wacce ake tuhuma Saratu Tukur Zaria ta musanta zargin da ake yi mata, Safeto Ahmed  ya ce " Ya mai shar'a, abin da ake tuhumar Saratu na ajiye Ramatu ya tabbata, muna rokon Kotu ta bamu dama mu gabatarda shaidu domin mu tabbatar da da'awan mu".


Bayan Alkalin Kotun ya gama rubutu bisa tsarin tanadin shari'a, Kotu ta ba mahaifin Ramatu belinta har zuwa ranar Juma'a 1 ga watan Nuwamba 2019. Amma Kotu ta tasa keyar Saratu zuwa Kurkuku har zuwa wannan ranar.

Sai dai wakilin Mujallar isyaku.com ya lura cewa da farko dai wannan shari'a an farata ne daga Kotun sharia ta 1 a garin Birnin kebbi, daga bisani ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba Alkalin Kotun ya tura shari'a zuwa babban Kotun shari'a mai daraja ta 1, wanda shi ma Alkalin bai bata lokaci ba ya tura shari'ar zuwa babban Kotun shari'a ta 4 a garin Birnin kebbi, bayan Kotunan baya sun bayar da hujja kan dalilan hurumi bayan sun yi la'akari da kalaman kara da aka rubuta a takardar FIR.

Haka zalika , wakilin Mujallar isyaku.com ya lura cewa babu jami'an hukumar Hizbah ko daya a wajen wannan shari'a duk da yake bayanai sun tabbatar cewa jami'an hukumar ne suka kai samame da ya yi sanadin kamo Saratu Tukur Zariya da Ramatu Muhammed.

Yayin da wasu manema labarai suka nemi jin ta bakin mahaifin Ramatu bayan an fito daga Kotu, watau Malam Muhammad Najega, wanda ke zaune a unguwar Tungar Zabarmawa a garin Jega, ya ki sauraren manema labarai, sai dai ya ce " Kada ka numa ni, ko fita zata yi a gida ana hadata da mai rakiya (escort a kalamansa) ba zan hana ku yi abin da za ku yi ba, amma kuma kuna da yara ".

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post