Tap di jan! Yaro dan shekara 11 ya yi wa budurwa cikin shege, karanta dalili


Legit Hausa

An tura wata mata gidan yari na tsawon shekara ashirin a birnin Florida, bayan an kamata da laifin yiwa yaro dan shekara 11 fyade har ta kai ga ta dauki ciki da shi.

Budurwar mai suna Marissa Mowry wacce keda shekaru 22, an dauke ta a matsayin wacce za ta dinga kula da yaron a shekarar 2014, inda ita kuma tayi amfani da wannan damar ta dinga lalata da yaron.

A yadda kotu ta bayyana, Marissa tayi lalata da wannan yaron ne a lokuta da dama ba tare da tayi amfani da wani abin kariya ba. A karshen shekarar 2014 din ta haifi jariri wanda yaron yayi mata cikin shi.

Sai dai yaron bai yi magana akan wannan abu ba sai a shekarar 2017, inda ya bayyanawa mahaifiyarsa, ita kuma ta tuntubi jami'an 'yan sanda, bayan anyi gwaji an gano cewa yaron shine mahaifin jaririn da Mowry take da shi sai aka kamata.

Yanzu haka dai Mowry tana da shekaru 28, inda shi kuma yaron yake da shekaru 17, shi kuma jaririn da suka haifa yanzu yana da shekara 5. Mahaifiyar yaron da aka yiwa fyaden ta bayyanawa manema labarai cewa abinda Mowry ta yiwa danta ya canja mishi rayuwa baki daya.

Ta ce dan nata wanda a yanzu haka shima dalibi ne, sai ya fara kai dan da aka haifa masa makaranta a kowacc rana kafin shi kuma ya wuce tashi makarantar.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari