A yi min afuwa, ban kammala ba aka kama ni - Magidanci da ya yi ma yar shekara 9 fyade


Legit Hausa
Wani mai siyar da ruwa dan shekara 30 da aka kama yana lalata yarinya yar shekara tara a Adamawa ya roki da ayi mai rangwame kan hujjar cewa “bai kammala” ta’asar ba kafin aka kama shi.

Mai laifin, Mohammed Babangida, wanda hukumar tsaro na NSCDC ta gurfanar a ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba, ya fada ma manema labarai cewa shi sabon shiga ne a wajen aikata laifin, sannan cewa yayi danasanin abunda ya aikata.

“Wannan shine karo na farko da na aikata hakan sannan banma kammala ba lokacin da aka kwankwasa kofana, inda hakan ya tursasa ni dakatawa.

“Ina roko da a yafe mun a matsayina na magidanci dake da yara. Ina zama a Bauchi; bana son wannan abun kunyan ya wargaza iyalina. Gaba daya abun ya fara ne wasu yan kwanaki da suka gabata lokacin da yarinyar ta roke ni N50 domin ta siya cincin, inda tayi ikirarin cewa tana jin yunwa, sai na bata.

“Sai ya kara dawowa ta roke ni kudi a wata rana san na bata N20; sai ta sake zuwa gidana na bata N50 sannan muka shiga daki,” inji Babangida.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post