An kammala Maulidin Sheikh Amad Tiijani a jihar Kebbi, karanta abin da ya faru

An kammala Maulidin Sheikh Ahmad Tijjani da Matasan Darikar Tijjaniyya suka shirya a jihar Kebbi, a harabar Masallacin Juma'a na unguwar Wala a tsohon garin Birnin kebbi wanda ya sami halartar jama'a daga fadin jihar Kebbi da kewaye ranar Asabar.

Kungiyar samari da matasan Darikar Tijjaniyya ta sha shiryawa tare da daukan nauyin Wa'azi, Maulidi, da Zikiri hadi da Lakca kan ababen da suka shafi addinin Musulunci da Darikar Sheikh Ahmad Tijjani a fadin jihar Kebbi kawo yanzu.

Maulidin ya sami halarcin manyan Malamai da suka hada da Sheikh Yusuf Zuru, wanda ya yi nasiha amadadin Dr. Abdullahi Umar Sa'ad Zuru, wanda ya bayar da "Tarihin Sheikh Ahmad Tijjani R.A".

Sai Dr. Sani Birnin Tudu, wanda Malam Aliyu Rimi Jega, ya yi jawabi a madadinsa kan "Minene Darika". Malam ya yi wadataccen jawabi kan manufofin Darikar Tijjaniyya tare da bayar da misalai da suka inganta a madogaran ilimi da lissafin hikima.

Sheik Mansur Imam Kaduna ya yi jawabi kan "Shari'a da Hakika" wanda ya ja hankalin dimbin mabiya Darikar Tijjaniyya da suka halara a wajen wannan Maulidi.

Sayyadi Muhktar Shehu Dahiru Usman Bauchi, ya yi jawabi a kan "Gudunmuwar Sufaye da Sufanci a Musulunci".

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN