An kama wasu matasa da ke yi wa matattu fashi a makabarta

Legit Hausa
'Yan sanda a jihar Ogun sun kama wasu matsa biyu; Emmanuel Aro, mai shekaru 25, da Anu Olofinju, mai shekaru 25, bisa zarginsu da farke kabarin wata mata tare da cire kokon kan ta a wata makabarta da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa.
Da yake tabbatar da kama matasan a ranar Lahadi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce an kama masu laifin ne biyo bayan korafin da wani mutum mai suna Amoo Bankole ya shigar a ofishin 'yan sanda da ke Eggua.
A cewar Oyeyemi, Bankole ya shigar da korafin cewa an ga matasan biyu na haka kabarin da aka binne mahaifiyarsa a 'ya watannin da suka gabata, kuma ya yi zargin cewa matasan na da wata mummunar manufa.
"Bayan samun korafin Bankole, DPO na ofishin 'yan sandan Eggua, SP Kehinde Oyekangun, ya tashi jami'an 'yan sanda domin su garzaya makabartar, su iske matasan, amma sai suka hadu da su a kan hanyarsu. Bayan an caje matasan ne sai aka gano kokon kan matar a cikin wata jakarsu," a cewarsa.
Kakakin rundunar 'yan sandan ya bayyana cewa mutumin da ya shigar da korafin ya tabbatar da cewa kokon kan mahaifiyarsa ne aka samu tare da matasan.
Ya kara da cewa matasan sun amsa laifinsu tare da bayyana cewa zasu yi amfani da kokon kan matar ne domin yin tsafin samun kudi.
Bashir Makama, kwamishinan 'yan sandan jihar, ya bayar da umarnin mayar da masu laifin sashen binciken manyan laifuka domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da su.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post