Legit Hausa
Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 62 ne suka rasa ransu
sannan da dama suka jikkata sakamakon wani harin bam da aka kaddamar ana tsaka
da sallar Juma'a, a Afghanistan.
Shafin BBC ta rahoto
daga wani shaida da lamarin ya afku a idonsa cewa karfin tashin bam din ya yaye
rufin gidaje da dama. Sai dai zuwa yan an tattaro cewa babu wani wanda ya dauki
alhakin kaddamar da harin.
Harin na zuwa ne bayan rahoton Majalisar Dinkin Duniya na
cewa adadin fararen hular da suka mutu a kasar ta Afghanista ya zarce tunani. A
cewar Majalisar Dinkin Duniya, an kashe yan farar hula 1,174 tsakanin watannin
Yuli da Satumba.
Attaullah Khogyani, mai magana da gwamnan lardin ya bayyana
cewa mutane 62 aka kashe sannan mutum 36 sun samu raunuka a harin da aka kai wa
masallata. Masallacin da aka kai harin ya kasance a gundumar Haska Mina,
kilomita 50 daga birnin Jalalabad.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp