Zargin tayar da hankalin Gwamna Bagudu, Kotu ta daga shari'ar matar da DSS ta kama

An ci gaba da sauraron karar da hukumar DSS rundunar jihar Kebbi ta shigar a babban Kotun Majistare mai daraja ta 1 a garin Birnin kebbi kan Aisha Zakari da Gwamnatin jihar Kebbi, bisa zargin cewa ta tayar wa Gwamnan jihar Kebbi da hankali ta wayar salula. Da misalin karfe 2:19 na ranar Alhamis, Aisha Zakari ta bayyana a cikin Akwatin wadanda ake tuhuma a cikin Kotu domin fuskantar tuhuma da DSS ke yi mata.

Latsa bidiyo a kasa 
Saidai Alkalin Kotun, ya kasa ci gaba da wannan shari'a domin Lauyan DSS D.I Namata, ya ce har yanzu hukumar tana gudanar da bincike a kan lamarin. Ya kuma nemi Kotu ta daga shari'ar zuwa mako uku nan gaba. Amma Lauyan Aisha Barista A.A Fingilla, wanda ya jagoranci Lauyoyi da ke kare Aisha Zakari da suka hada da Barista Sale Muhammad Sale da Barista T.E Owoeye ya shaida wa Kotu cewa ya kamata a ce hukumar DSS ta kammala bincike kawo yanzu.

Fingilla ya gaya wa Kotu cewa DSS ta kama Aisha ne daga garin Yauri, kuma hanya bata da kyau, haka zalika Aisha tana shayar da karamar yarinya yar wata biyar a Duniya, sakamakon haka ya bukaci Kotu ta sa rana ta karshe da hukumar DSS za ta kammala bincike da ta ce tana yi kan lamarin domin ba Kotu dama ta fara shari'ar.

Daga karshe, Alkalin Kotun ya ba Lauyan hukumar DSS wata daya, domin kammala bincike, kuma Lauyan Aisha ya aminta da matsayin Kotu na bayar da wata daya domin DSS ta kammala bincike.

Daga bisani Majistaren Kotun ya daga shari'ar har zuwa ranar 29 ga watan Oktoba 2019 domin a fara shari'ar gadan gadan.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post