Yadda mutum 7 yan gida daya suka yi mutuwan ban mamaki lokaci daya

Tsoro da fargaba ya cika mazauna Mafoluku da ke unguwar Oshodi a birnin Ikko watau Lagos da safiyar yau, bayan an wayi gari an ga wani iyalin mutum bakwai 6 tare da wata bakuwa duk sun mutu.

Mai gidan tare da matarsa, da yaransu hudu har da wata bakuwa mai dauke da juna biyu sun mutu gabadayansu, bayan an gano haka da misalin karfe 10 na safiyar yau a gida mai lamba 19 da ke unguwar Olowora.

Bayanai sun ce ana zargin cewa iyalin sun ci abinci mai guba ne. An shaida wa jami'an yansandan Makinde, kuma sun  dauke gawakin mamatan daga gidan.

DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Latsa nan ka sami lambar yan mata masu bukatar aure 
Previous Post Next Post