Wata mata ta banka ma wani mutum wuta saboda bashin N200

Wata mata ta zuba ma wani mutum petur daga bisani ta banka masa wuta wai domin ya ki ya biyata bashi da take binshi na naira dari biyu N200.

Mr Sunday Arigbe, ya gamu da ajalinsa ne bayan wata mata da ake kira Faith mai shekara 42, ta watsa masa petur kuma wata mai sayar da petur ta kesta masa ashana sai wuta ta rufe Sunday sakamakon haka ya mutu.


Mujallar ISYAKU.COM ta samo  cewa lamarin ya faru ne dakarfe 2 na dare ranar 26 ga watan Augusta a mahadan titi na Arorfe und Jakpa da ke Effun a karamar hukumar Uvwie na jihar Delta.


Sai da yansanda sun damke Faith yayin da mace mai sayar da petur ta tsere.

DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post