Wata Jarumar Kannywood ta yi barazanar ficewa daga masana'antan sabodo rikicin siyasa


Legit Hausa

A irin kace nacen da ake ta faman samu dangane da kama fitaccen mawakin nan Nazir Ahmad Sarkin wakar San Kano, mutane da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan lamari da ya faru da mawakin.

Wannan dalili ne yasa Jaruma Teema Makamashi jakadiyar FKD tayi wani bidiyo cikin nuna alhini inda ta nuna bacin ranta akan kama Nazir din da aka yi har ta yi ikirarin ita ma ta kusa tabi sahun abokanan sana'arta da suka fice daga kungiyar shirya fina-finai ta Kannywood saboda ta gaji da abinda ke faruwa a masana'antar.

"Assalamu Alaikum, kamar dai yadda kuka sani sunana Teema Makamashi, yau kuma da abinda Kannywood ta wayi gari dashi kenan, ni sai yau nake ji wai an kama Nazir Sarkin waka, shugaban hukumar tace fina-finai a yiwa Nazir Sarkin waka adalci a sake shi.

 "Wannan abu da ake yi ko ba dan siyasa bane za ace saboda siyasa ne, saboda mun zo mun shiga siyasa mun zake, sun zo sai raba kawunan mu suke su suna can suna samun kudade, mu munzo wajen da muke cin abinci a nan za a tsaya kullum ana fada, babu ranar da garin Allah zai waye ba ayi wani abu a Kannywood ba.

"Wallahi gaskiya na kusa na bar Kannywood, ba zan iya wannan masifar ba, a yiwa Nazir Sarkin Waka adalci a sake shi, duka 'yan kwankwasiyya ake ta kamawa, 'yan APC din basa laifi ne, tunda aka fara wannan abun ba a taba kama dan APC ba, an jera hotunan jarumai biyar ance za a kamasu, kuma duk 'yan PDP ne."

Haka shima Jarumi Ali Nuhu ya fito ya roki hukumar da tayi sassauci akan wannan lamari, inda ya roketa da ta yiwa jarumin adalci ta sake shi .
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

 https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN