Wani yaro daga Ibadan ya Musulunta a Central Mosque Birnin kebbi

Wani yaro mai suna Tosin ya amshi kalmar Shahada na shiga addinin Musulunci a babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi watau Central Mosque ranar Juma'a. Tosin ya canja sunansa zuwa sunan addinin Musulunci watau Usman.

Limanin Masallacin , Imam Muhktar wanda shi ne Walin Masarautar Gwandu a jihar Kebbi ,ya karanta wa Usman kalmar Shahada kuma ya amsa. Daga cikin sahun shaida wannan babban aiki har da Wazirin Gwandu, Mataimakin Limamin Masallacin da sauran manyan mutane.

Usman ya fito daga garin Ibadan na jihar Oyo a kudancin Najeriya, kuma yana sana'a tare da Mahaifiyarsa a Tashar mota da ke gabas daga Asibitin Sir Yahaya a garin Birnin Kebbi.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post