Uwa da yayanta 2 sun mutu bayan sun ci abinci, uban na cikin mawuyacin hali

Legit Hausa
Wata uwa mai shekara 45 da yaranta biyu sun mutu a ranar Asabar bayan sun ci tuwon albo wanda aka fi sani da Amala mai dauke da guba a Odo-Ayedun Ekiti da ke karamar hukumar Ikole na jihar Ekiti.
Shekarar babban dan nata 14 yayinda karamin ke da shekara 12 a duniya.
An tattaro cewa mijin ne ya kawo garin albon yayinda matar kuma ta tuka suka ci.
An gano dukkanin ahlin da suka ci abincin kwance babu rai bayan sun kammala cin abincin dare, illa mahaifin wanda ke cikin mawuyacin hali a babban asibitin koyarwa na rayya da ke Ido Ekiti.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, tace an tsinci gawawwakin wasu karnuka biyu da suka ci guggubin garin a gidan.
An tattaro cewa makwabta wadanda suka shiga alhini bayan gano lamarin sun sanar da yan sanda.
Dan majalisa mai wakiltan Ikole II a majalisar dokokin jiar Ekiti, Hon. Adeoye Aribasoye ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a ranar Alhamis a Ado Ekiti.
Aribasoye ya kuma gabatar da lamarin gaban majalisa inda yayi kira ga a binciki lamarin.
Da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, DSP Caleb Ikechukwu ya tabbatar da lamarin.
Yace yan sanda za su hada hannu da sauran hukumomi domin binciken abunda ya haddasa mutuwarsu.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN