Tirkashi! Yadda wata mata ta yanke mazakutan mijinta da wuka

Wata mata mai suna Victoria Frabutt yar shekara 56, ta yanke al'auran mijinta Mr. Frabutt dan shekara 61 bayan ta daure shi daram a yanayi na killacewa, daga bisani ta yanke mazakutansa da wuka.

Shugaban yansanda masu bincike Chief Detective Jason Wank, ya ce , "Mun sami kira ne da karfe 4 na asuba a wani gida da ke Newport, Carolina na arewa (Kasar Amurka), sai muka tarar da matar Frabutt ta killace shi kuma ta daure shi, daga bisani ta yanke mazakutansa. Mun dauki guntun mazakutan muka dora a kan kankara sai muka garzaya da shi asibiti bisa tunanin ko likitoci za su yi kokarin hada mazakutan".

Yansandan sun kama Victoria kuma suna gudanar da bincike, daga bisani majiyar yansanda ta ce za su gurfanar da ita gaban Kotu.

Babu wani bayani kan dalilin da ya sa Victoria ta aikata wannan aiki.
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post