• Labaran yau

  Rikicin Gwamnatin jihar Kebbi da Aisha: Umar Namashaya Diggi na shirin jagorantar sulhu

  Bayan Gwamnatin jihar Kebbi karkashin Gwamna Atiku Bagudu ta sa an kama wata matar aure da ke shayar da jaririya yar wata biyar a Duniya mai suna Aisha Zakari daga garin Yauri na kudancin jihar Kebbi bisa zargin cewa ta tayar masa da hankali ta sakon Text, wanda hukumar tsaro ta DSS ta yi kuma ta gurfanar da Aisha a gaban Kotu. Mujallar isyaku.com ta samo cewa, wani dan kishin jihar Kebbi Alhaji Umar Namashaya Diggi, tsohon shugaban karamar hukumar mulki ta Kalgo ya dukufa wajen ganin an yi sulhu tsakanin bangarorin guda biyu marmakin ci gaba da kalubalantar juna a Kotu, tsakanin Gwamna da talaka matar aure mai shayar da jaririya.

  Latsa kasa ka saurari sauti:   Latsa nan ka sauke sautin murya

  Sai dai ita Aisha ta musanta tuhumar da ake yi mata a gaban Kotu. Lauyanta Barista A.A Fingilla ya shigar da kara a wata babban Kotun tarayya da ke garin Birnin Kebbi yana neman Gwamnatin jihar Kebbi tare da hukumar DSS su biya Aisha Zakari da Mijinta Nasiru Jatau Naira Miliyan dari biyar, sakamakon abin da ya kira cin zarafi na kamawa tare da tsare ma'auratan har kwana goma sha uku (13) tare da babban dansu ba tare da Gwamnati da DSS sun gurfanar da su a gaban Kotu ba.

  DAGA ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

  https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rikicin Gwamnatin jihar Kebbi da Aisha: Umar Namashaya Diggi na shirin jagorantar sulhu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });