Kalubalantar Gwamnan Kebbi a wayar salula: DSS ta kama maigida,matarsa mai shayar da yar wata 6

Wani faifen sauti da muka samu a Mujallar isyaku.com, ya nuna yadda wata baiwar Allah ta koka kan yadda ake zargin cewa jami'an tsaro na Department of State Services watau DSS, runduna ta jihar Kebbi, ta kama wani mutum a garin Yauri Alhaji Nasiru, da karfe daya na dare, tare da matarsa Aisha Nasiru, wacce ke renon yarinya mai wata shida a Duniya mai suna Khadijat, tare da Babangida babban dan Alhaji Nasiru tun ranar Asabar 31 ga watan Agusta 2019.

Mai bayani a sautin, ta yi zargin cewa, an kama wadannan ma'aurata ne a unguwar Sabuwar Tasha da ke garin Yauri, bisa zargin cewa an zagi Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ta wayar salula, lamari da ya sa jami'an tsaro suka dau mataki bayan an alakanta yin haka ga Aisha matar Nasiru yayin da shi kuma Alh. Nasiru ake zargin cewa yana zagin Atiku Bagudu a kafar sada zumunta na Facebook.

Yunkuri da muka yi domin jin ta bakin hukumar DSS  na jihar Kebbi ya ci tura, domin hukumar bata da Kakaki ko mai magana da yawunta a jihar Keebi, hakazalika mun kasa samun Daraktan hukumar na jihar Kebbi kawo yanzu da muka wallafa wannan rahotu.

Latsa kasa ka saurari sauti:



DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN