KDF ta bukaci gwamnatin jihar Kebbi ta fuskanci matsalolin talakawa da suka fi sayen Mitoci

Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Iliyasu Bashar yayin jawabinsa na karbar gaisuwar Juma'a a Fadar Abdullahi Fodio da ke garin Birnin kebbi ranar Juma;a ya ce,wajibi ne Gwamnati da KEDCO su zauna a ci wa matsaya dangane da lamarin Mitan lantarki kan ko kyauta ne ya kamata a ba mutane Mita.

Saidai a nashi jawabi, Sakataren kungiyar cigaban jihar Kebbi watau Kebbi Development Forum (KDF) Alhaji Usman Abubakar Gwandu, ya ce KDF tana lurar da gawamnatin jihar Kebbi kan harkar sayen Mitoci domin a rarraba wa jama'a. Abubakar ya ce ko da an yi haka ba abu ne da zai ci gaba ba, domin gwamnati tana da ababe da ya kamata ta mayar da hankali a kansu ba wai ta azurta wani kampani mai zaman kanta ba.


Abubakar ya ce " Gwamnati tana da matsaloli da ya kamata ta tunkara marmakin ta zo tana azurta kampani mai zaman kanta".
Ya kara da cewa " Tun farko dai bamu yarda ba a saida wadannan mitoci , shi yasa muka rubuta wa National Electricity Regulation Commission NERC, da kuma Ministan albarkatun kasa da wutan lantarki, domin a fayyace mana , domin mun san gwamnati ta ce kyauta za a bayar da su.kamar yadda tsohon Ministan harkar wutan lantarki ya fada".

Yan shekarun baya dai, KEDCO ta samar wa masu anfani da wutan lantarki wadannan Mitoci kyauta,aka kuma sa masu kyauta, amma sai kuma yanzu aka ce saye za'a yi a kan kudi har Naira dubu talatin da takwas N38.000 fuska daya ko naira dubu saba'in N70.000 mai fuska biyu ko uku.. 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

 https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post