Kama Aisha: An maka Gwamna Bagudu da DSS Kotu domin neman diyyan Miliyan 500

Lauyoyin mutuni da hukumar DSS rundunar jihar Kebbi ta kama Nasiru Jatau tare da matarsa Aisha Zakari daga garin Yauri na jihar Kebbi ranar 1 ga watan Satumba, kuma rundunar ta gurfanar da Aisha mai shayar da yarinya yar wata biyar a Duniya a gaban Kotun Majistare 1 a garin Birnin Kebbi bisa zargin cewa ta tayar wa Gwamanan jihar Kebbi Atiku Bagudu hankali sun kammala shirin gurfanar da hukumar DSS tare da wasu manyan jami'an Gwamnatin jihar Kebbi gaban wata babban Kotun tarayya a garin Birnin kebbi.

Latsa kasa ka saurari Barista Fingilla:Barista  A.A Fingilla shugaban ofishin Lauya mai zaman kansa Adalci Law chambers, ya shaida mana cewa sun shirya tsaf domin gurfanar da Gwamnatin jihar Kebbi tare da hukumar DSS bisa zargin  cin mutunci da taka hakkin bil'adama da Gwamnatin jihar Kebbi tare da hukumar DSS suka yi ma Nasiru  Jatau tare da matarsa Aisha Zakari.

Barista Fingilla ya ce suna bukatar Kotu ta sa Gwamnatin jihar Kebbi tare da hukumar DSS su biya Nasiru Jatau tare da matarsa Aisha Zakari Naira Miliyan dari biyar N500,000.000 kuma Gwamna Atiku Bagudu da Daraktan DSS na jihar Kebbi su nemi gafarar Nasiru da Aisha a bainar jama'a da kuma a kafofin yada labarai, hakazalika Lauyan ya bukaci Kotu ta hana Gwamna Bagudu tare da hukumar DSS sake kama Nasiru Jatau ko matarsa Aisha kan wannan zance.

Latsa nan ka sauke sautin murya >>>Barista A.A Fingilla yana bayani kan shigar da kara Kotu


DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post