Legit Hausa
Alkalin kotun ya soke dukkan bukatar da hukumar gudanar da
zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta gabatar na watsi da karar jam'iyyar PDP da
Atiku Abubakar. Hukumar INEC ta bukaci kotun zaben ta yi watsi da karar PDP
saboda daya daga cikin lauyoyinta, Dakta Livy, ba sahihin lauya bane.
Hakazalika INEC ta bukaci kotu ta soke bukatar PDP da Atiku
na cewa shugaba Buhari bai cancanci yin takara a zabe ba. Misalin karfe 30,
Alkalan kotun zaben shugaban kasa karkashin jagorancin Alkali Garba Muhammad,
sun zauna kuma komai ya kankama. Shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole;
ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, Shugaban ma'aikatan fadar
shugaban kasa, Abba Kyari, ministan kwadago, Cris Ngige; tsohon gwamnan jihar
Bauchi, Mohammed Abubakar, sun isa kotun.
Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, lauyoyin jam'iyyar
PDP, Dakta Livy, Mike Ozekome, sun isa kotu. Daga cikin wadanda ke kotun akwai,
gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; tsohon
shugaban EFCC, Nuhu Ribadu. Kawo yanzu, lauyoyi biyu sun isa kotun; Cif Charles
Edosomwan na jam'iyyar APC, da kuma Sam Ologunoria na hukumar INEC.
Rana ba ta karya, sai dai uwar da taji kunya - Allah ya kawo
mu ranar 178 bayan kammala zaben shugaban kasa a ranar 23 ga Febrairu, 2019
inda hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman ta INEC ta alanta shugaba
Muhammadu Buhari matsayin wanda ya lashe zaben.
Bayan sanar da sakamakon zaben, jam'iyyar PDP da HDP sun
shigar da kara kotun zaben shugaban kasa domin kalubalantar wannan sakamako.
Daga baya, jam'iyyar HDP da dan takararta suka janye kararsu daga kotun bisa
wasu dalilai, amma PDP ta ce sam sai ta ga abinda ya kwancewa kura zani.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN