Gwamnan jihar Zamfara ya amince da dawo da malaman makaranta 556 da gwamnatin Yari ta kora

Legit Hausa
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da maido da malaman makaranta 556 da gwamnatin da ta gabata ta kora.
Hakan na kunshe ne a cikin takardar da babban daraktan yada labarai na jihar, Yusuf Idris ya sa hannu kuma ya mika ga manema labarai a Gusau ranar Juma'a.
Ya ce tuni gwamnan ya umarci shugaban ma'aikatan jihar da a fara biyan albashin ma'aikatan a watan Satumba.
Matawalle, ya jinjinawa malaman akan hakurinsu da juriya akan lamarin kuma ya horesu da su kasance masu dabi'a ta gari yayin da suka dawo aikin gwamnatin jihar.
Ya ce dawo da su aiki na daya daga cikin burikan gwamnatinsa na sauraro da kuma share kukan masu koke.
A cikin satin ne malaman makarantar 556 suka kai kokensu ga gwamnan inda a take ya umarci shugaban ma'aikatan jihar, Kabiru Balarabe da ya tantance ingancin koken tare da nagartaccen rahoto akan haka.
Bayan binciken shugaban ma'aikatan ya nuna cewa akwai inganci a maganganunsu, sai gwamnan ya amince da dawo dasu bakin aikinsu.
Idan zamu tuna, gwamnan ya dawo da ma'aikata 1,040 cikin 1,400 da gwamnatin Yari ta dauka aiki amma aka ki biyansu albashi har na watanni 18.
Ma'aikatan da abin ya shafa sun bukaci hakkinsu ta hanyar maka gwamnatin a kotu inda suka yi nasara.
DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN