APC ta sha babban kaye a wata jiha bayan an dawo da dan majalisa na PDP da kotun zabe ta tsige

Legit Hausa
Kotun daukaka kara dake zama a Akure a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba, ta sauya hukuncin kotun kararrakin zabe wacce ta soke zaben Hon. Ikengboju Gboluga na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a matsayin mamba mai wakiltan mazabar Okitipupa/Irele a majalisar wakilai.
Kotun sauraran karan zaben ta soke nasarar Gboluga a watan Yuli, bisa rantsuwar biyayya ga kasar Birtaniya, bayan ya karbi shaidan zama dan kasar.
Kotun ta kuma bayyana Albert Akintoye na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Febrairu, 2019.
Ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta ba Akintoye takardan shaidar lashe zabe bayan ta janye takardan shaida daga Gboluga.
Amman a wani hukuncin da aka zartar, alkalai uku na kotun daukaka kara M.A Danjuma, R.M Abdullahi da P.A Mahmood sun yanke hukuncin cewa bai cancanci a soke haifaffen dan kasar Najeriya ba a takaran zabe ba don saboda ya kasance da karin takardan shaidan wata kasa wanda yayi rantsuwar zai yi ma biyayya.
Saboda haka kotun daukaka karan ta soke hukuncin kotun zaben sannan ta karfafa zaben Ikengboju Gboluga a matsayin wanda zai wakilci al’umman mazabar Okitipupa/Irele a majalisar wakilai na kasa.
Kotun har ila yau ta daura ma Albert Akintoye dan takaran APC taran naira miliyan 2. Ta kuma ce dole a biya kudin kafin ranar 1 ga watan Oktoba, 2019.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN