Legit Hausa
Gwamnan jahar Ekiti, ya bayyana dalilin zuwansa kasar Afirka
ta kudu yayin da ake samun tashin tashinan hare haren kin baki bakaken fata a
kasar wanda hakan yayi dalilin mutuwar bakaken fata da dama, tare da asarar
dukiya mai yawa.
Jaridar Premium Times ta ruwaito Fayemi ya bayyana cewa ba
wai ya je Afirka ta kudu da nufin halartar taron tattalin arziki na duniya
wanda Najeriya ta janye daga zuwa bane, a’a, yace ya tafi kasar ne don halartar
taron Stellensbosch wanda wani dan jaridar Najeriya, Dele Ollojede ya
gayyaceshi ne.
Haka zalika majiyar Legit.ng ta ruwaito mai martaba Sarkin
Kano, Muhammadu Sunusi tare da gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai
duk sun halarci wannan taro na Stellensbosch ne ba wai taron tattalin arzikin
ba.
Yan Najeriya da dama sun bayyana bacin ransu biyo bayan
watsuwar hotunan mutanen 3 a kasar Afirka ta kudu, a daidai lokacin da
gwamnatin Buhari ta yi ma jakadan kasarta kiranye daga Afirka ta kudu bisa
rikicin daya kaure, don haka suke ganin ya kamata su ma su ma su dakatar da duk
abinda suka je yi a kasar don nuna ba’a tare.
Fayemi ta bakin kaakakinsa Olayinka Oyebode ya bayyana cewa
Dele Olojede ne ya gayyaceshi don halartar taron kirkire kirkiren fasaha ta
duniya, kuma ya gudana ne a wani yanki dake na tazara sosai daga Cape Town inda
ake taron tattalin arzikin kasa. “Babban abin ma shi ne an kammala taron tun
kafin gwamnatin ta sanar da janyewa daga taron tattalin arziki na duniya.” In
ji shi.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN