DA DUMINSA: Kotun zabe ta yi watsi da karar Atiku da PDP


Legit Hausa

Bayan kwashe akalla sa'o'i takwas ana zaman kotu kan shari'ar dake tsakanin shugaba Muhammadu Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP, shugaban kwamitin Alkalan kotun, Mohammed Garba, ya yi watsi da karar da PDP da Atiku suka shigar. Kotun zabe ta yanke hukuncin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci yin takaran kujeran shugaban kasa saboda yana da kwalin karatun da ake bukata har fiye da haka.

Kotun zaben shugaban kasa ta yi watsi da zargin cewa dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ba haifaffan dan Najeriya bane kuma bai cancanci takaran zabe. Kotun ta yi watsi da ikirarin jam'iyyar PDP da Atiku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da yan sanda da sauran jami'an tsaro wajen magudin zabe. Kotun ta ce akwai tafka da warwara saboda ta yaya PDP da Atiku za suce jami'an tsaro sun yi magudi kuma su manta da su lokacin shigar da kara kotu.

Alkalin kotun ya soke dukkan bukatar da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta gabatar na watsi da karar jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar. Hukumar INEC ta bukaci kotun zaben ta yi watsi da karar PDP saboda daya daga cikin lauyoyinta, Dakta Livy, ba sahihin lauya bane. Hakazalika INEC ta bukaci kotu ta soke bukatar PDP da Atiku na cewa shugaba Buhari bai cancanci yin takara a zabe ba. Misalin karfe 30, Alkalan kotun zaben shugaban kasa karkashin jagorancin Alkali Garba Muhammad, sun zauna kuma komai ya kankama.

Shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole; ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ministan kwadago, Cris Ngige; tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, sun isa kotun. Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, lauyoyin jam'iyyar PDP, Dakta Livy, Mike Ozekome, sun isa kotu.

Daga cikin wadanda ke kotun akwai, gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu. Kawo yanzu, lauyoyi biyu sun isa kotun; Cif Charles Edosomwan na jam'iyyar APC, da kuma Sam Ologunoria na hukumar INEC. Rana ba ta karya, sai dai uwar da taji kunya - Allah ya kawo mu ranar 178 bayan kammala zaben shugaban kasa a ranar 23 ga Febrairu, 2019 inda hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman ta INEC ta alanta shugaba Muhammadu Buhari matsayin wanda ya lashe zaben.

Bayan sanar da sakamakon zaben, jam'iyyar PDP da HDP sun shigar da kara kotun zaben shugaban kasa domin kalubalantar wannan sakamako. Daga baya, jam'iyyar HDP da dan takararta suka janye kararsu daga kotun bisa wasu dalilai, amma PDP ta ce sam sai ta ga abinda ya kwancewa kura zani.


DAGA ISYAKU.COM

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post