Da dumi dumi: Tsohon shugaban kasa ya rasu a kasar Saudiyya

Legit Hausa
Tsohon shugaban kasar Tunisia na mulkin kama-karya, Zine El-Abidine Ben Ali ya rigamu gidan gaskiya a kasar Saudiyya inda ya tsere domin neman mafaka tun a shekarar 2011, kamar yadda jaridar Aljazeera ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ben Ali ya rasu ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba yana dan shekara 83 bayan doguwar jinya da ya yi fama da ita a wani babban asibiti dake kasar Saudiyya.
Lauyansa, Mounir Ben Salha ya tabbatar da mutuwar Maigidan nasa, inda yace: “Yanzun nan Ben Ali ya rasu a kasar Saudi Arabia.” Haka zalika shima ministan harkokin kasashen wajen Tunisia ya tabbatar da mutuwar Ali.
A watan Janairu na shekarar 2011 ne Ben Ali ya arce daga Tunisia biyo bayan wata babbar zanga zanga da al’ummar kasar suka gudanar suna bukatar ya sauka daga mulki bayan kwashe shekaru 23 yana mulkin kasar, mulkin zalunci, mulkin mallaka kuma mulkin kama karya.
Wannan zanga zanga ta faru ne bayan wani karamin dan kasuwa Sidi Bouzid ya banka ma kansa wuta ya kashe kansa sakamakon bacin rai daya dameshi bayan jami’an tsaro sun kwace masa dan baron da yake kasa kayansa a ciki yana sayarwa.
Ko a ranar lahadin da ta gabata sai da aka gudanar da zaben shugaban kasa a karkashin tsarin dimukradiyya a kasar Tunisia, inda daga cikin wadanda suka tsaya takarar akwai wani dan gani kashenin Ben Ali, Abir Moussi, wanda ya samu kashi 4 na kuri’un da aka kada.
A shekarar 1987 Ben Ali ya kwace mulki daga hannun tsohon shugaban kasar Habib Bourguiba wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa na dindindin, watau shugaban kasa na mutu ka raba, amma Ben Ali ya kawar da shi bayan ya bayyana ma duniya cewa Habib ba shi da lafiya.
Masana sun tabbatar da cewa duk da zaluncin da ake zargin Ben Ali da shi a zamaninsa, amma an samu gagarumar cigaban tattalin arziki a kasar, wanda hakan yasa wasu yan kasar suke ta kukan ya dawo bayan an hambarar da gwamnatinsa sakamakon halin matsin tattalin arziki da suka tsinci kansu a ciki.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN