Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamna Sanata Atiku Bagudu Akan Kalubalen Zahiri Ga Mutane

20th September, 2019

Zuwa Ga
Mai Girma Gwamna

Da Farko, Ina Rubuta Wannan Wasika Ba Saboda Ni Kadai Ba, Ina Rubutawa Ne A Madadin Abokan Zamanmu Da Suke Da Bukata Ta Musamman, Ingantattun Mutanen Jihar Kebbi, Da Suke Tambayata Akan Magana Akan Bukatunsu.

Mai Girma Sanata Atiku Bagudu Ina Farin Ciki Kasancewata Anan, Dan Asalin Jihar Kebbi, Kuma Mazauni Tsakanin Mutanen Kirki Na Hadaddiyar Kungiya. Abinda Yaja Hankalina Tare Da Yan Uwana, Mutane Masu Bukata Ta Musamman A Wannan Jihar, Sun Dauki Shekaru Da Dama, Koda Yaushe Ina Bukatar Ganinsu Cikin Nutsuwa Kuma Mutane Masu Daraja, Musamman Wadanda Suke Da Wani Mataki A Karatu.

Shin Yallabai Kasan Kuwa, Shekara Guda Da Ta Wuce Ranar 29 Ga Watan February 2018, Mai Girma Sanata Osita Izunaso Tare Da Gidauniyar Kpakpando Suka Amsa Mana, Yan Nigeria Da Kalubalensu A Disapora, Aka Samu Nasarar Tsara Gabatar Da Babbar Tattaunawa Ta Farko, Shugaban Majalisar Dattijai Wanda A Ranar 28 Ga Watan March 2018 Ya Nemo Wasu Bayanai Da Ya Rasa, Wanda Suka Ci Karo Da Mutane Masu Nakasa, Doka A 2018 Da Kuma Yin Zabe Cikin Nutsuwa, Kamar Yadda Sanata Izunaso Yayi Alkawari, Da Kuma Mambobinmu Na Nigeria Akan Kusoshin Kalubale.

1. Ina Tunanin Mutum Daya Ya Kalli Mutane Nawa Ne Tuntuni Suke Da Nakasa, Ina Tunanin Wannan Zai Gyara Wasu Abubuwan. Nakasa Bata Nufin Gazawa, Gwamantinka Ya Kamata Ta Nuna Goyon Baya Wajen Nisanta Masu Roko Akan Titi, Da Kuma Marasa Aikin Yi.

2. Muna Bukatar Tallafin Karatu A Ciki Da Wajen Kasar Nan, Ga Wasu Nakasa Domin Cigabansu, Domin Bunkasa Iliminsu, Da Kuma Samun Hidima Mafi Inganci Ga Mambobinmu.

3. Nakasa Ba Abin Alhaki Bace, Mafi Yawa Daga Cikinsu Suna Gudanar Da Mabanbamtan Kasuwanci Tare Da Kwarewarsu, Zamu Yi Farin Ciki Idan Ka Samo Hanyoyin Samar Musu Da Hanyoyin Da Zasu Samu Damammaki.

4. Abinda Yankinmu Yake Bukata, Imma Daga Dan Doka (Wato Wakili A Zauren Majalisa) Imma Kuma Daga Zababbe Ko Bangaren Shari'a, Manomi, Dan Kasuwa Ko Ma'aikacin Lafiya. Yayin Da Muka Hadu Guri Guda, Zamu Daga Darajar Mutanenmu, Da Kuma Tura Matsayinsu Gaba Domin Samun Rayuwa Mai Inganci.

5. Muna Rokonka Ka Nada Mataimaki Na Musamman Ta Bangaren Masu Bukata Ta Musamman A Gwamantinka, Ko Kuma Ka Kirkiri Wani Tsari A Ma'aikatar Harkokin Mata Da Cigaban Jama'a. Dukda Cewa Rahoto Ya Same Mu Cewa Kayi Shiri Akan Wasu Bukatun.

6. Lamarin Bara, Musamman A Tsakanin Masu Wata Lalura A Jikinsu, Yana Kasancewa Kalubale A Gwamnatoci Da Yawa. Bangaren Arewacin Kasar Nan Yana Bayyana Yadda Abin Yayi Muni, Wanda Bara Ta Samu Kusan Hanyar Rayuwar Wadansu Mutanen A Jihohin Arewa. Gwamnatin Jiha Ta Bangaren Samun Walwalar Tsaron Jama'a, Ya Zama Dole Ta Taimaki Mutane Masu Lalura A Jikinsu, Domin Su Dogara Da Kansu, Kuma Subar Yin Bara A Titi.

7. Mu Na Musamman Ne, Muna Bada Himma Domin Kokarin Cimma Kawar Da Talauci Ga Mutanenmu, Ta Hanyar Karfafa Musu Gwiwa A Shirye Shiryen Ilimi, Da Daukaka Darajarsu Wajen Basu Tallafi, Domin Mayar Dasu Masu Dogaro Da Kansu.

8. Yallabai Ina Fatan Samun Farin Ciki Akan Kananan PWDs A Fadin Jihar Kebbi, Wanda Kyatuttuka Na Musamman A Duniya.

Ina Roko Akan, A Shirye Muke Mu Hada Hannu Dakai, Wajen Tunanin Tsarin Tafiyar Da Gwamantinka Da Shirye Shiryenka, Wanda Zasu Bayyana Bukatu Na Mutane Masu Nasara A Jikinsu.

Muna Da Tabbas Akan Zaka Bijiro Da Shirye Shirye Masu Amfani, Domin Mutanenmu Su Amfana.

Khalied Aliyu Papa Yauri

0/Post a Comment/Comments

Rubuta ra ayin ka

Previous Post Next Post