An yi wa Zainab bulala 80 bisa aifin shan tabar wiwi a jihar Kaduna

Legit Hausa
Wata kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a unguwar Magajin Gari ta jihar Kaduna, ta yanke wa wata budurwa masi shekaru 19 a duniya, Zainab Abdullahi, hukuncin bulala 80 biyo bayan kama ta da laifin shan tabar wiwi a bainar al'umma.
Da yake zartar da hukuncinsa a ranar Alhamis, Alkalin kotun Malam Muhammad Shehu Adamu, ya zartar da wannan hukunci a kan Zainab bayan ta amsa laifin da ake zarginta da aikata wa na shan tabar wiwi a filin Allah.
A rahoton da jaridar The Punch ta ruwaito, Alkali Shehu ya ce bulala 80 shi ne hukuncin da shari'a tayi tanadi ga duk wanda aka akama da laifi makamancin wanda Zainab ta aikata na shaye-shayen kayan maye.
Ya gargadi kungiyar musulmi ta Najeriya, MCN, a kan ta ci gaba ayyuka na gari da ta saba kuma tayi kokari wajen ladabtar da Zainab domin koma wa hanyar gaskiya.
Jami'i mai shigar da kara a gaban kotu, Ibrahim Shu'aibu, ya bayar da shaidar cewa jami'an tsaro na 'yan sanda ne suka cafke Zainab a yayin da take tsaka da zukar tabar wiwi a kan titi.
Kamar yadda Shu'aibu ya bayyana a gaban kotu, an taba kama Zainab da laifi kuma tayi zaman gidan Dan Kande a sanadiyar gaza biyan kudin tara na N7,000 da aka shimfida a kanta har zuwa lokacin da kungiyar MCN ta fito da ita bayan ta biya tarar da ke rataye a wuyanta.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN