An kama 'yan gargagiya 9 da suka kai hari wuraren ibada a jihar Ogun

Legit Hausa

Akalla bayan kimanin wata guda da wasu 'yan addinin gargajiya suka kai hari wani masallaci a yankin Idi-Iroko na karamar hukumar Ipokia ta jihar Ogun, a karshen makon da ya gabata an sake kai wa mabiya addinin Islama da na Kirista hari a yayin bukukuwan al'ada na Oro.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ana tattaro cewa 'yan gargajiyar Oro sun sanya wa al'ummar Idi Iroko dokar takaita zirga-zirga, inda mabiya addinin Islama da kuma na Kirista suka yi watsi da dokar domin fitowa wuraren gudanar da ibadunsu, lamarin da yayi sanadiyar kai masu hari.

Rahotanni sun bayyana cewa, da yawa daga cikin mabiya addinin Islama da kuma na Kirista wadanda suka yi wa dokar 'yan gargajiyar kunnen uwar shegu, sun kwashi kashin su a hannu inda aka lakada masu dukan tsiya da mummunan cin zarafi.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, Tolahat Yahya, ya ce baya ga lakada masu dukan tsiya da 'yan gargajiyar Oro suka yi a sanadiyar sabawa dokar takaita zirga-zirga da suka shimfida a yankin, sun kuma yi wa motarsa ta hawa mummunan lahani.

Sai dai Yahya ya ce sun samu nasarar cafke uku daga cikin maharan inda suka danka su a hannun hukumar 'yan sanda.

Da yake zantawa da manema labarai, limamin babban masallacin Idi Iroko na Umar bin Khattab, Abdulazeez Omoakin, ya ce sabanin hare-haren baya inda ba a ko taba lafiyar mutane, a yanzu yan gargajiya sun kai wa masallata hari na kwanton bauna kuma sun yi masu jina-jina.

A yayin bayar da tabbacin aukuwar wannan hari, hukumar 'yan sanda reshen jihar Ogun, ta ce ta cafke wasu daga cikin 'yan gargajiyar 90 da suka hadar da; idowu Desu, Monday Akinlolu, Dele Dada, Raimi Jacob, Dondo Sunday, Abiola Azeez, Olarewaju Akerele, Nurudeen Lawal da kuma Tetede Jamiu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce ababen zargin 9 da aka cafke sun shiga hannu ne a yayin da suke tsaka da aikata wannan mummunar ta'asa.


0/Post a Comment/Comments

Rubuta ra ayin ka

Previous Post Next Post