Yanzu-yanzu: Obasanjo yana ganawar sirri da shugabanin kungiyoyin Fulani

Legit Hausa
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya na ganawa da shugabanin kungiyoyin Fulani da ke zaune a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
An kira taron ne domin warware matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a yankin da galibi ake zargin fulani da alhakin kai hare-hare.
Shugabanin Fulanin sun isa wurin taron ne karkashin jagorancin, Saleh Bayeri, shugaban kungiyar Gan Allah Fulani Association da wasu shugabani uku da ke wakiltan jihohin Kudu maso Yamma da jihar Kogi.
Obasanjo ya iso wurin taron tare da wani da aka ce makiyaya sun taba kai wa hari.
A jawabinsa na bude taro kafin su kebe, Obasanjo ya shawarci mahalarta taron su fadi dukkan abinda ke zuciyarsu domin hakan ne kawai za a samu maslaha
"Ina rokon ku da kada ku bar wani abu a zuciyarku, ta hakan ne kawai za mu iya samun nasara a wannan taron.
"Dukkan mu mun san halin da kasar ke ciki na rashin tsaro. Ya kamata su nemo hanyoyin warware matsalar," inji shi.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post