Yanzu Yanzu: Kungiyar Shi’a ta shigar da kara domin kalubalantar hukuncin gwamnatin tarayya na haramta ayyukantaLegit Hausa

Kungiyan yan uwa Musulmai na Shi’a wato Islamic Movement in Nigeria (IMN) ta shigar da kara domin kalubalantar hukuncin haramta ayyukan kungiyar da gwamnatin tarayya tayi.

A cikin karar, kungiyar Shi’a ta bukaci kotu da ta janye umurnin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli na bayyana kungiyar IMN a matsayin kungiyar yan ta’adda.

Idan za ku tuna gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da haramta ayyukan kungiyar Shi’a a karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem El-zakzaky. Mohammed Adamu, sufeto janar na yan sanda, ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Talata, 30 ga watan Yuli.

Wata kotun tarayya da ke Abuja ta kaddamar da kungiyar a matsayin kungiyar ta’addanci, biyo bayan wani kara da gwamnatin tarayya ta shigar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar da ke kare hakkin Musulmi (MURIC) a ranar Litinin, 29 ga watan Yuli ta mara wa Gwamnatin Tarayya baya akan haramta ayyukan kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wanda aka fi sani da Shi’a da kuma kaddamar da ita a matsayin kungiyar ta’adda.

MURIC ta bayyana matakin a matsayin kudurin da zai karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya. 


DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post