Yanzu-yanzu: An gwabza fada tsakanin matasan Hausawa da na Yarbawa a kudancin Najeriya

An yi asarar miliyoyin dukiya sakamakon wani tashin hankali da ya auku da safiyar Lahadi a kasuwar Oke-Odo da ke birnin Ikko watau Lagos tsakanin matasan Hausawa da na Yarbawa.

Majiyarmu ta ce ba a san musabbabin wannan tashin hankalin ba, amma dai an tafka mumunar asarar dukiya na miliyoyin naira. Hakazalika majiyar ta ce rikicin ya fara ne tun ranar Asabar, sai kuma ya fadada ranar Lahadi.

An kuma yi harsashen cewa mutane da dama ne suka samu raunuka daban daban sakamakon tashin hankalin.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post