Yan jam'iyar APC guda 12,562 sun yi wa jam'iyar zindir a jihar Zamfara

Legit Hausa

Fiye da y’ay’an jam’iyyar APC 12, 562 ne suka yi wankan tsarki suka tunjuma cikin jam’iyyar PDP, kuma suka samu kyakkyawar tarba daga gwamnan jahar Zamfara, Gwamna Bello Matawalle. Gwamnan ya karbi dubun dubatan yayan jam’iyyar ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta a garin Gusau, wanda daga cikinsu akwai tsofaffin kwamishinoni guda uku da suka hada da Alhaji Idris Keta, Alhaji Abdulkadir Ahmed da Alhaji Aliyu Tsafe.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sauran sun hada da tsofaffin shuwagabannin kananan hukumomi da suka hada da Alhaji Musa Tsafe da Alhaji Ahmed Kantoma, da wasu tsofaffin manyan daraktoci Alhaji Bashir Kwaren Ganuwa da Alhaji Saminu Lawali. Da suke gabatar da jawabansu, Alhaji Idris Keta da ALhaji Habibu Alo sun bayyana cewa abin da ya ja hankalinsu zuwa jam’iyyar PDP shi ne zaman lafiyar da ake samu a jahar Zamfara a mulkin Matawalle bayan tsawon lokaci ana fama da matsalar tsaro.

Manyan yan siyasan biyu sun bayyana cewa shawo kan matsalar da gwamnan ya yi yasa ya samu aminci daga jama’an jahar, don haka su ma zasu bashi goyon baya don cigaba da tabbatar da tsaro a kasar. Da yake nasa jawabin, Matawalle ya bayyana cewa yan siyasa sun yanke hukuncin daya kamata da shigowa jam’iyyar PDP, kuma ya basu tabbacin ba zai nuna bambanci tsakaninsu da tsofaffin yan jam’iyyar ba.

Haka nan gwamnan ya tabbatar da cigaba da kokarinsa na tabbatar da tsaro a jahar Zamfara, tare da inganta rayuwar mutanen da hare haren yan bindiga ya shafa, sa’annan yace gwamnati za ta samar da wani tsari na kulawa da yan gudun hijira. Daga karshe gwamnan ya bayyana cewa sun samu goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da taimakonsa don mayar da yan gudun hijiran zuwa gidajensu nan bada jimawa ba.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post