Yan bindiga sun kashe mataimakin Chiyaman na jam'iyar APC

An yi wa mataimakin shugaban jam'iyar APC na mazaba ta 5, a karamar hukumar Oyigbo na jihar Rivers Edward Okechukwu kisan gilla bayan wasu yan bindiga sun bude masu wuta suka kashe shi tare da wasu mutum hudu da safiyar Litinin.
 
Yan unguwar da lamarin ya faru sun yi zargin  cewa maharan sun fito ne daga Ilori na al'umman Ogoni da ke karamar hukumar Tai a jihar Rivers.
 
Hakazalika maharan sun kai harin ne da mugan makamai kamar su bindiga kirar AK47, kuma suka yi mumunan ta'addi ga dukiyar al'umma da suka kai wa harin.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post