Yadda wasu samari 4 suka mutu wajen ceton wata mace da aka sace ( Hotuna)

Wasu mutane da ake kyautata zaton cewa yan fashi ne sun sace wata mace mai suna Mercy Gabriel ranar Talata 13 ga watan Agusta bayan ta fito daga shagonta da ke kusa da shataletalen Ankpa reshen Obu da ke Otukpa a karamar hukumar Ogbadibo a jihar Benue.

Bayanai sun ce macen da aka sace ta kammala aikin bautan kasa NYSC a jihar Kogi, wata da ta gabata. Hakazalika majiyarmu ta ce masu satan mutane sun turata zuwa cikin motarsu suka arceda ita.

Sai dai wani ganau ya ce nan take bayan lamarin ya faru, sai wasu matasa guda hudu suka hau babura suka bi barayin a guje, amma yayin tsere da babura domin su ci ma motar barayin mutanen, sai wata mota ta bugesu kuma suka mutu nan take kuma aka kai gawakinsu a Asibitin Otukpa, yayin da masu satan mutanen suka tsere lafiya kalau tare da macen da suka sace.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post