Ya kamata gwamnati ta yi wa Zakzaky adalci - Shugaban Izala Bala Lau


Legit Hausa


Jagoran kungiyar Izala ta Najeriya JIBWIS (Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Ikamatis Sunna), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya shawarci gwamnatin Najeriya da cewar ya kamata ta yiwa jagoran 'yan shi'a Sheikh Ibrahim Zakzaky adalci.

Shawarar babban malamin addinin na Islama ta zo ne a yayin da yake gabatar da hudubarsa ta Juma'a a masallacin babbar cibiyar kungiyar JIBWIS da ke Utaku cikin birnin Abuja a ranar Juma'a 2 ga watan Agusta. Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, wannan ba shi ne karo na farko ba da wani babban malamin addinin Sunnah a kasar ya sa baki game da sha'anin jagoran 'yan shi'a da ke tsare a hannun gwamnati tun a shekarar 2015.

Sheika Bala Lau ya ce: "Babu wanda ba ya son a yi wa shugabansu (Zakzaky) adalci. Ko kafiri ne a yi wa adalci. Idan abin da ya yi ba daidai ba ne a hukunta shi saboda gani ga wane, ya isa wane tsoron Allah." "Idan ba a yi masa hukunci ba zanga-zanga da tawaye za su sa a sake shi. Idan kuwa aka sake shi to ranar da duk aka kama wani shugaba na kowane addini mabiyansa su ma su fito su yi zanga-zanga, su yi abin da suka ga dama domin a saki shugabansu.

"Daga nan babu sauran zaman lafiya kenan," a cewar sa. Kazalika, ya ce "idan jagoran 'yan Shi'an bai yi laifi ba, to a sake shi. Idan ko ya yi laifi a yi masa hukunci kamar yadda ake yi wa kowane dan kasa mai laifi. "Idan aka yi haka an zauna lafiya." Ya ce: "Akwai wasu da suke kokarin yin amfani da matsalar wajen hada 'yan Izala fada da 'yan Darika a Najeriya. Suna cewa idan aka gama da 'yan Shi'a su za a koma wa." Shehin malamin ya kuma kara da cewa yadda wasu ke kokarin siyasantar da batun jagoran na shi'a ya na ci masa tuwo a kwarya.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post