Wata mace mai matakin karatu Digiri da ke siyar da abinci a Baro, duba nawa take samu

Yayin da rayuwa ke zuwa ga kowane bil'adama ta yadda Allah yake so ta kasance ga bawansa, ya rage ga dan Adam ya fuskanci kalubalen rayuwarsa, wannan wata mace ce mai suna Jossy Otu mai shaidan karatu mataki na Digiri, amma fa take zagayawa gari tana sayar da abinci a cikin Baro duk da yake tana da aure.

Jossy ta ce " Da farko ina jin kunyan yin wannan sana'a musamman ranar farko da na fita tallan siyar da abinci da Baro, amma daga bisanisai na saba. Na sami ribar Naira dubu dari da hamsin N150.000 a cikin kwana sittin 60 watau wata biyu 2 da na fara sana'ar".

Josse dai tana auren wani Lauya ne amma haka bai hanata tashi tsaye domin taimakon kai da kai ba ga iyalinta.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post