Wata budurwa ta rataye kan ta saboda ta yi cikin shege


Legit Hausa

Jami'an 'yan sanda sun samu gawar wata matashiya, Ilona Grant, mai shekaru 23, wacce ta rataye kan ta a gidanta bayan ta gano cewa tana dauke da juna biyu. Ilona ta kashe kan ta be kwana daya bayan ta sanar da saurayinta cewa tana dauke da juna biyu, kuma tana son zubar da shi.

 Jami'an 'yan sanda sun samu gawar Ilona a rataye a gidanta da ke unguwar Neath a yankin Port Talbot a kudancin Wales bayan makwabtanta sun kira su. Makwabtan Ilona sun kira jami'an 'yan sandan ne da safiyar ranar 6 ga watan Agusta bayan sun ji tana daga murya yayin musayar yawu da sauarayinta a ranar 5 ga watan Agusta.

Kwana daya kafin ta kashe kan ta, Ilona ta ziyarci kwararren da ke duba ta, saboda tana da matsala a kwakwalwar ta, tare da sanar da shi cewa dauke da juna biyun wata guda, kuma tana son zubar da shi. Lamarin da yasa mai duba lafiyar ta ya kira saurayint tare da sanar da shi halin da ake ciki.

Ana zargin cewa Ilona ta fasa kwalbar giya a jikin bango tare da yi wa kan ta rauni kafin daga bisani ta rataye kan ta, kamar yadda jami'an 'yan sanda suka sanar bayan sun isa gidan da ta rataye kan ta. Mai kula da matsalar Ilona, Colin Philips, ya ce matashiyar ta kashe kan ta ne saboda rashin isashiyar kulawa da goyon bayan da take bukata
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post