Wani tsohon dan Majalisan wakilai a jihar Kebbi ya aikata wani abun tarihi ga jama'arsa

Tsohon dan majalisan wakilai na tarayya wanda ya wakilci Birnin kebbi, Kalgo da Bunza a zauren Majalisan Wakilai na tarayya Hon. Abdullahi Muslim, ya sake ba jama'arsa mamaki bayan ya tallafa wa Mata da tahunan nika guda arba'in, ya kuma tallafa wa matasa da tahunan ban ruwan aikin gona guda arba'in wanda ya kawo adadin tahuna tamanin kenan da Muslim ya raba domin tallafa wa jama'a.

Latsa kasa ka saurari sauti:Mujallar isyaku.com ya tattaro cewa wannan aiki ne a karkashin shirin tallafa wa matasa na shekaran 2018, amma duk da yake baya kan kujerar mulki, Abdullahi Muslim ya saukar da nauyi na amana da jama'a suka damka masa ta hanyar idar da ayyukansa ga talakawan amana da suka zabe shi cikin yanayi na tsabta domin ya wakilce su a zauren Majalisan tarayya.


DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post