Wani karamin yaro dan Boko Haram ya gwada yadda aka koya masa harbi da sarrafa bindiga (Hotuna)


Legit Hausa

Wani karamin yaro dan kungiyar Boko Haram da aka kama ya gwada yadda aka basu horon harbi da bindiga da kuma sarrafa makami yayin yaki. Yaron, wanda bai wuce shekaru 15 ba a duniya, ya gwada yadda ake rike bindiga da saka harsashi da kuma harba ta. Kazalika, ya nuna irin yadda ya kamata mutum ya tsaya ko tsuguna wa yayin da yake rike da bindiga.

Kungiyar Boko Haram na amfani da kananan yara maza da mata wajen kai hare-hare a jihar Borno, musamman wajen kai harin kunar bakin wake. Ko a yau (Laraba), sai da wasu kananan yaran mata guda biyu yan kunar bakin wake suka tayar da bama bamai a jahar Borno, inda suka kashe mutane guda uku, sa’annan suka raunata wasu mutane Takwas, inji rahoton jaridar Guardian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Borno, SEMA, Bello Danbatta ya bayyana cewa yan kunar bakin sun kai harin ne da yammacin Talata da misalin karfe 8:30 na dare a yankin Mafa. Boko Haram sun shafe kusan shekara 10 kenan suna yaki da gwamnatin Najeriya da nufin kafa daular Musulunci a Najeriya, kuma suna amfani da kananan yara musamman mata wajen kai harin kunar bakin wake a masallatai, kasuwanni, gidajen kallo, teburin mai shayi, da kuma tashoshin mota.
 

DAGA ISYAKU.COM

 Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN