Rikon amana: Wani tsohon dan majalisa a jihar Kebbi ya yi abin da ya ba jama'a mamaki

Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya Hon. Abdullahi Muslim, ya kai taimakon kayakin karatu da ya jibanci kimiyya ga Makarantar pramare na garin Gulumbe a jihar Kebbi. Abdullahi Muslim ya wakilci Birnin kebbi, Kalgo da Bunza a Majalisar wakilai na tarayya.

Latsa ka saurari sauti a kasa:Duk da yake ya sauka daga kujerar mulki, Abdullahi Muslim ya bi diddigin wani shiri da shugaba Buhari ya bayar da umurni a yi, kuma daf da zai sauka mulki aka sa hannu a wannan aiki da ya cika alkawari a yau bayan ya sha Safa da Marwa domin ganin wannan aiki ya tabbata tare da sauran ire irensu.DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post