Tirkashi: Wani dan majalisa ya takarkare ya banka tusa a dakin majalisa da ta sanya kowa ficewa daga dakin

Legit Hausa
Wani dan majalisa da ya banka tusa a dakin majalisa ya yi sanadiyyar da ya sanya dole aka rufe dakin majalisar kasa Kenya, yayin da 'yan majalisar suka fara zargin junansu akan warin tusar.
Dan majalisar da ba a san ko waye bane, ya banka tusar a dakin majalisar Homa Bay a ranar Larabar nan da ta gabata, bayan dan majalisa daya daga cikinsu ya zargi dan uwansa da yin tusar.
A yadda rahoto jaridar DailyMail ya nuna, dan majalisar da ake zargin ya karyata zargin da ake yi masa, inda ya bayyana cewa babu yadda za ayi yayi irin wannan abin kunyar a gaban abokanan aikinshi.
Cikin gaggawa kakakin majalisar ya bukaci a kawo turare wanda zai kawo saukin warin tusar.
Wannan tusa dai ta yi sanadiyyar da ya sanya aka daga taron majalisar na tsawon minti goma, yayin da kakakin majalisar ya bayyana cewa ba zai yiwu su cigaba da zama a cikin wannan wari ba.
Idan ba a manta ba a cikin satin nan ne aka kori wata 'yar majalisa ta kasar ta Kenya daga dakin majalisar saboda ta shiga da jaririyarta.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post