Ta kwabe wa barayi da yanmatansu da suka yi ma wata budurwa fashi a cikin mota

Yansanda a jihar Anambara sun cafke wasu matasa biyu da yanmata biyu Bayan sun yi ma wata mata fashin Jakarta da ke dauke da kudi.

Bayanai sun ce matar mai suna Filomina yar shekara 30 ta shiga mota ne tare da wadannan mutane daga Akwuzu zuwa Ntaje da ke karamar hukumar Oyi.

Amma bayan suna cikin tafiya ne sai wàdannan bata gari suka kula cewa Filomina tana dauke da kudi a cikin Jakarta. sai suka tsayar da mota cewa ta dan fita za su dan sassauta kujerar mortar.

Saukarta ke da wuya sai suka ja mota suka gudu da Jakarta da ke dauke da N400.000, sakamakon haka matar ta yi ta kuwa har aka sami wadanda suka bi su da abin hawa har yansanda suka kamasu.

DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post