Sunaye: Buhari ya yi wa manyan sakatarorin ma'aikatun tarayya canjin wurin aiki


Legit Hausa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a ya yi wa wasu manyan sakatarorin ma'aikatun gwamnatin tarayya da Akantanci sauyin wuraren aiki sakamakon kirkiran sabbin ma'aikatu da aka yi. Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa a ranar Laraba yayin rantsar da sabbin ministoci, Shugaban kasar ya sanar da kirkiran sabbin ma'aikatu buyar.

Ma'aikatan sun hada da Ma'aikatan Ayyukan Talafawa Al'umma, Ma'aikatan Jin Kai da Agajin Gaggawa, Ma'aikatan 'Yan sanda, Ma'aikatan Ayyuka na Musamman da Kasashen Waje sai ma'aikatan Sufurin Jiragen Sama.

A cewar sanarwar da Mrs Olawunmi Ogunmosunle, Dirketan Yadda Labarai na Ofishin Shugaban Ma'aiktan Gwamnatin Tarayya ta fitar a ranar Juma'a a Abuja, Shugaban Ma'aika Mrs Winifred Oyo-Ita ta rattaba hannu kan sanarwar sauyin wurin aikin. Wani sashi na sanarwar ya ce, "Duba da kirkiran sabbin ma'aikatu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, wadannan jami'an za suyi aiki a matsayin babban sakatare ko Akanta.

"Wadanda abin ya shafa sune Mr Daudu - Babban sakatare, Ma'aikatan Ayyuka na Musaman, Mr Louis Edozien – Babban sakatare, Ma'aikatar Makamashi, Mr Mbaeri Nnamdi – Babban sakatare, Ma'iakatan Ayyukan 'Yan sanda, Dr Mahmoud Isa-Dutse – Babban sakatare, Ma'aikatan Kudi. “Dr Muhammed Dikwa – Babban sakatare, Kudi zuwa (Ayyuka na Musamman), Mr Ernest Umakhire – Permanent Secretary, Kudi (Kudi da Tsare tsaren tattalin arziki),

Mrs Anagbogu Nkiruka – Babban sakatare, Ma'aikatan Harkokin Mata, Alh Sabiu Zakari – Babban sakatare, Ma'aikatan Sufuri. “Dr Mohammed Bukar – Babban sakatare, Ayyuka da Gidaje, Mr Hassan Musa – Ma'aikatan Sufurin Jiragen Sama, Direkta (Hukumar Sufurin Jiragen Sama) zai kula da ofishin Babban sakatare.

“Mrs Anetu-Anne Ajiu, Direkta, Kula da Walwalan Al'umma, Ma'aikatan Mata da yyukan Cigaba, Ma'iakatan Ayyukan Jin Kai (Direkta, Ayyukan Walwalan Al'umma) zai kula da ofishin Babban sakatare.” A cewat Oyo-Ita, sauya-sauyan za su fara aiki nan take kuma za su cigaba da kasancewa hakan har zuwa nan gaba.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post