Sowore: Atiku ya yi magana kan kama dan takarar shugaban kasa da DSS ta yi

Legit Hausa
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai ta kama wasu 'yan Najeriya biyu da ake zargin jami'an hukumar DSS ta aikatawa a ranar Juma'a da Asabar kan yawan cacakar gwamnati da su keyi.
Mutane biyun da aka kama dai sune Omoyele Sowore, dan gagwarmaya kuma mawallafi jaridar Sahara Reporters da kuma Abubakar Idris, malamin jami'a kuma dan Kwankwasiyya da ya dade yana cacakar tsare-tsaren Gwamna Abdullahi Ganduje da Shugaba Muhammadu Buhari.
Atiku ya rubuta a shafinsa na Twitter a safiyar Asabar: "Kudin tsarin mulkin kasar mu ta bawa kowa damar fadin ra'ayinsa, wannan shine ginshikin demokradiyar mu. Na yi tir da wannan 'satar mutanen' da aka ce wai kame ne".
An kama Sowore ne misalin karfe 1.30 na daren Juma'a a gidansa da ke Legas kuma wani hadiminsa da suke tare ya ce jami'an SSS ne suka kama shi suka tafi da shi ofishinsu da ke Shangisha a Legas.
Matar Abubakar Idris ta shaidawa manema labarai cewa wasu mutane dauke da manyan bindigogi sun yi gaba da shi a lokacin da ya ke kokarin shiga gida bayan ya dawo daga tafiya misalin karfe 1.00 na daren Alhamis.
A na zargin cewa wadannan mutanen jami’an tsaro ne da na hukumar DSS masu dauke da fararen kaya. Wannan abu ya faru da Abu Hanifah wanda a ka fi sani da Abubakar Dadiyata ne a gidansa da ke cikin Garin Kaduna.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post