Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnoni da manyan yan APC a Daura (hotuna)


Legit Hausa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnonin APC da sauran manyan masu ruwa da tsaki a Daura, jihar Katsina a ranar Talata, 13 ga watan Agusta. Manyan jiga-jigan jam’iyyar mai mulki sun kai wa Shugaban kasar gaisuwar babban sallah ne a gidansa da ke mahaifarsa na Daura.

Gwamnonin a suka hallara sun hada da na jihar Katsina, Aminu Bello Masar; gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi; gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo Olu; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da kuma gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki Sauran manyan masu ruwa da tsakin da suka hallara sun hada da Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari; Shugaban NITDA, Isa Ali Pantami da kuma mukaddashin Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, da dai sauransu.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post