Masu taimako sun sace kudin wanda mota ta buge suka gudu suka barshi cikin jini


Legit Hausa

Wani matashin saurayi da hatsarin mota ya ritsa dashi a Ikorodu dake jihar Legas ya bayyana cewa mutanen da suka je domin su taimakesu sun sace mishi kudin dake cikin aljihunshi.

A yadda rahoton ya nuna, hatsarin ya faru ne yayin da tayar mota ta cire taje ta bige wani mutumi a lokacin da yake tafiya akan babur.

Wannan dalili ne yasa mutane suka yi dafifi domin su dauke daga kan babbar hanyar wacce motoci ke faman kai kawo, amma kuma a yayin da mutanen ke kokarin dauke mutumin, wani da ba a san ko waye ba ya sanya hannunsa a cikin aljihunshi ya dauke mishi kudi kimaninm naira dubu takwas.

Wannan lamari dai bai yiwa mutumin dadi ba, domin kuwa duk da irin ciwon da yaji bai sa barawon ya tausaya masa ba, ya sakaya hannu ya zare masa dan kudin da yake riritawa.

Wannan abu da ya faru ba shine na farko ba, saboda ya sha faruwa a lokuta da dama idan hatsari makamancin haka ya faru a kasar nan.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post