Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da belin tsohon Shugaban INEC kan N1bn

Legit Hausa
Babban kotun tarayya dake Ikoyi ta bada belin tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Maurice Iwu, akan naira biliyan daya.
An gurfanar da Farfesa Iwu ne bisa laifuffuka hudu da suka hada da boyewa, zamba da karkatar da kudi har naira biliyan 1.2.
A karar, hukumar EFCC tayi zargin cewa Farfesa Iwu ya taimaka wajen boye kudaden ne tsakanin Disamba 2014 da Maris, 2015.
Kudin yana daga cikin N23.29b da ake zargin tsohuwar Ministar man Fetur, Diezani Allison-Madueke ta raba don yin magudi a zaben shugaban kasa na 2015.
Sai dai kuma Farfesa Iwu ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa akai, sannan kuma lauyansa, Ahmad Raji (SAN) ya bukaci kotu da ta bashi beli akan dalilan da suka shafi sanin kai da kuma sassaucin ra’ayi.
Lauyan mai kara, Rotimi Oyedepo, a nashi bangaren yace akwai shaida da ke nuna yiwuwar razabar da wadanda za su bayar da shaida idan har aka bashi beli, kuma saboda haka ya bukaci kotu da ta yi amfani da ikon ta taki bashi beli.
Bayan sauraran muhawara daga bangarorin biyu, Justice Chuka Obiozor ya ba da belinsa, inda ya bukaci a kawo wadanda za su tsaya masa mutum biyu, sannan kuma ya hana Iwu yin magana da shaidun guda biyu.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post