Komai ya kankama domin shillawar Zakzaky Indiya (Hotuna)


Legit Hausa

Komai ya kankama domin tafiyar shugaban kungiyar IMN wanda akafi sani da Shi'a, SheikIbrahim El-Zakzaky, kasar Indiya domin jinya biyo bayan belin da kotun jihar Kaduna ta bashi a makon da ya gabata. Mun kawo muku rahoton cewa an tafi da Sheik Ibrahim Zakzaky birnin tarayya Abuja.

El-Zakzaky zai tafi Indiya tare da matarsa Zeenat inda za su nufi Asibitin Medenta dake New Delhi a kasar ta Indiya domin a duba lafiyarsu. Wata majiyar IMN dake Kaduna ce ta sanar da wakilin Daily Trust wannan labarin inda ta ce, jagoran na IMN yanzu haka yana Abuja tare da jami’an tsaron DSS inda yake jiran tashinsu zuwa Indiya a wani karamin jirgin sama.

A yanzu haka, Sheikh Zakzaky da iyalinsa suna babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja kuma zasu tashi da jirgin Emirates misalin karfe 6 daidai.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post