Kebbi: Yansanda sun kama yan banga 6 da suka kashe mutum 2 a Fakai


Rundunar yansandan jihar Kebbi ta kama wasu yan banga guda shida bisa zargin kashe wasu da ake zargin masu sace mutane ne domin karban kudin fansa a cikin jihar.

Kwamishinan yansandan jihar Kebbi Mr. Garba Danjuma ne ya shaida wa manema laabarai haka a Birnin kebbi ranar Talata.

Ya ce yan banga da aka kama da suka fito daga kauyen Kainji, a gundumar Mahuta da ke karamar hukumar Fakai, sun kama wasu mutum biyu, Muhammad Dankarami da Muhammad Buda da ke kauyen Maidangwami da ake zargin cewa masu sace mutaane ne.

Ya kara da cewa wadanda yan bangan suka kama basu sami damar kare kansu ba domin yan bangan basu basu dama ba sai yan bangan suka kashesu, daga bisani kuma jama'a suka kone gawarsu

Hakazalika ya ce rundunarsa ta damke yan banga da suka yi wannan kisa kuma sun amsa laifinsu.
DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post