Kungiyar KDF jihar Kebbi ta bayar da muhimmiyar shawara gabanin zaben kananan hukumomi

Kungiyar da ke yekuwa domin fadakarwa kan ci gaban jihar Kebbi KDF, ta gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki a garin Birnin kebbi ranar Laraba inda aka tattauna kan ababe da dama da suke iya zama kalubale ga zabukan kananan hukumomi da ke tafe da kuma yadda za'a magance su.

Arc. Lawal  Muhammad Yusuf ya yi jawabin karshen taro, tare da takaita gabadayan jaddawalin taro, da kuma lissafta ababen da suka zama kalubale ga samun nassara wajen zaben kananan hukumomi da salon siyasa domin amfanin jama'ar jihar Kebbi

Saurari sautin ababen da aka gano da yadda ake shirin fuskantar kalubale: Profesa M.D Mahuta, shugaban KDF, da Sakataren KDF Alh.  Usman Abubakar Gwandu, sun gabatar da jawabai da suka jibanci kalubale da yadda za'a magance su bisa maudu'in taron.Haka zalika wasu masu ruwa da tsaki a kungiyar ta KDF, sun gabatar da jawabai kan maudu'in taron tare da gano matsaloli da kuma bayar da shawarwari kan yadda za a magance su.

Wasu daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai sun hada da:

1.Garba Abubakar Besse- Jigo a siyasar jihar Kebbi
2.Muhammad Lawal Abubakar - Sakataren kungiyar ASUSS
3.ACG Sambo Gwandu - Marafan Gwandu
4.Ibrahim Muhammad - KCC
5.Shitu Musa Tela - Babban dan Jarida
6.Abdullahi Ibrahim - Janar Manaja, GM Vision FM Birnin kebbi
7.Madam Balkisu Atuna Danga - Shugaban NCWS reshen jihar Kebbi.
8.Hauwa Abubakar Zaki - Daga kungiyar FOMWAN reshen jihar Kebbi
9.Yahaya Sarki - Wakilin jaridar Leadership sashen Turanci, jihar Kebbi

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post