Legit Hausa
Taura John Paden, mawallafin littafin "Muhammadu
Buhari: Kalubalen mulki a Najeriya" ya lissafa dukkan 'ya'yan shugaban
kasa, Muhammadu Buhari, da makarantun da suka halarta tun daga firamare har
zuwa jami'a.
1. Fatima: An haife ta a shekarar 1975. Ta halarci
makarantar firamare ta 'ya'yan sojojin sama a Victoria Island, Legas. Ta
halarci makarantar sakandire ta 'Government College, Kaduna. Ta yi karatun digiri
na farko a jami'ar ABU, Zaria, kafin daga bisani ta wuce jami'ar kasuwanci ta
Stratford da ke kasar Ingila inda ta yi digiri na biyu.
2. Nana Hadiza: An haife ta a shekarar 1981. Ta fara karatu
a makarantar 'Essence International School da ke Cobham Hall, Kent, Ingila. Ta
yi karatun jami'a a jami'ar Buckingham da ke kasar Ingila. Ta yi karatun
diflomar malaman makaranta a Kaduna, sannan ta yi karatun digiri na biyu a
'Polytechnic Kaduna (KADPOLY)'.
3. Safinatu: An haife ta a shekarar 1983. Ta fara karatu a
makarantar 'Essence International Schools; Cobham Hall, Kent, a kasar Ingila.
Ta yi karatun digiri na farko a jami'ar Plymouth da ke kasar Ingila kafin daga
baya ta koma jami'ar Arden da ke kasar Ingila domin ilimi mai zurfi.
4. Halima: An haife ta a shekarar 1990. Ta fara karatu a
makarantar International Schools da ke Kaduna kafin daga bisani ta halarci
British School Of Lome a kasar Ingila. Ta halarci makarantar 'Bellerby's
College' da ke Brighton a kasar Ingila daga nan kuma ta wuce jami'ar birnin Leicester
a kasar Ingila, sannan ta dawo gida Najeriya inda ta halarci makarantar horon
lauyoyi da ke Legas.
5. Yusuf: An Haifa shi a shekarar 1992. Ya fara karatu a
'Kaduna International school, daga nan kuma ya wuce zuwa 'British school of
Lome. Kazalika ya halarci makarantar 'Bellerby's College, Brighton' a kasar
Ingila kafin daga bisani ya halarci jami'ar Surrey a kasar Ingila.
6. Zahra: An Haifa ta a shekarar 1994. Ta fara karatu a
'Kaduna International school, daga nan kuma ta wuce zuwa 'British school of
Lome. Kazalika ta halarci makarantar 'Bellerby's College, Brighton' a kasar
Ingila kafin daga bisani ta halarci jami'ar Surrey a kasar Ingila.
7. Aisha (Hanan): An haife ta shekarar 1998 kuma ta fara
karatu a 'Kaduna International School' 8. Amina (Noor): An haife ta a shekarar
2004. Ta fara karatu a makarantar a 'Kaduna international school'
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi