Hoton karya da ke yawatawa don tsangwaman jama'ar kasar Zuru

Wannan hoto ya dade yana zagayawa shafukan sada zumunta bayan wasu ma'abuta amfani da kafofin sada zumunta musamman na Facebook suka dinga amfani da hoton suna cewa mutanen Zuru ne a karamar hukumar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi.

Mujallar isyaku.com ya tattaro cewa wannan hoto ba a kasar Zuru aka dauke shi ba kuma ba mutanen kasar Zuru bane a hoton. Amma ake zagayawa da hoton bisa wata manufa da ke dauke da kulliyar raini da neman tayar da fitinan kabilanci da nuna bangaranci ga jama'ar kasar Zuru na kudancin jihar Kebbi suka dade suna fama da shi a hannun wasu Hausawan jihar Kebbi.

Yayin da tsofaffin Gwamnonin mulkin farar hula na jihar Kebbi kamar Adamu Aliero, ya jawo yan kasar Zuru a lokacin mulkinsa ba tare da nuna bangaranci ko banbanci ba. Wanda sakamakon irin wannan adalci har yanzu yana tare da tsohon mai bashi shawara kan harkar watsa labarai, watau Abdullahi Zuru.
Haka zalika, a lokacin mulkin tsohon Gwamna Sa'idu Nasamu Dakingari, wanda bafulatani ne dan kasar Dakingari, ya damka lamurran harkokin kananan hukumomi ga mataimakinsa K. Aliyu, wanda haka ya sa jama'ar kudancin jihar Kebbi da suka kunshi Masarautar Zuru da Yauri suka amfana ta hanyar cin gacin alfarmar siyasa da ke kunshe da wannan ma'aikata.

Sai dai wani abin tausayi shi ne yadda Gwamna Atiku Bagudu da ke kan kujerar mulkin jihar Kebbi ya kasa mika wa mataimakinsa Samaila Yombe Dabai ko da wata ma'aikata daya balle jama'ar yankinsa su ci gajiyar wannan hadaka da aka yi tsakanin kudancin jihar Kebbi da suka fitar da mataimakin Gwamna a karkashin jam'iyar APC, da kuma Kebbi ta tsakiya da suke da kujerar Gwamna.

An sha ganin mataimakin Gwamna Samaila Yombe yana wakiltar Gwamna Bagudu a wasu lamurra a jihar Kebbi, wanda ya kunshi wakilci kan taro daban daban, zaman majalisar jiha, da dai sauransu. Amma majiyarmu ta ce Yombe baya da iko kan asusu ko baitulmalin jihar  Kebbi  kamar yadda doka ta shata, amma Gwamna zai iya kayyade masa iya abin da zai iya sa hannu ya fitar idan baya cikin jiha. Wannan ma babu tabbatacin cewa Gwamna Bagudu ya ba Yombe wata dama koda na taba Miliyan daya idan baya nan.

Mujallar isyaku.com ya tattaro cewa kasar Zuru tana da jama'a da aka shaide su da gaskiya da aiki tukuru, hakuri, ladabi da biyayya a kowane hali da yanayi maza da matansu, kuma sakamakon haka wasu Hausawa ke auren matan Zuru saboda ladabi da biyayya ga miji.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post